Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci da ke kauyen Yandoto, ƙaramar hukumar Tsafe, inda suka halaka mutum biyar yayin da ake sallar asuba a safiyar Juma’a.
Daily Trust ta rawaito cewa shaidun gani da ido sun ce maharan sun kutsa cikin masallacin ne suka fara harbi ba kakkautawa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar nan take tare da jikkata wasu da dama.
Wani mazaunin garin ya ce bayan haka, maharan sun kuma yi awon gaba da wasu daga cikin masu sallar.
A cewar rahotan, wadanda suka samu rauni suna karɓar kulawar likitoci a asibiti, kuma an ce wasu daga cikinsu na samun sauƙi.
Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya shaida cewa har zuwa lokacin da aka tuntube shi bai samu rahoton faruwar lamarin daga babban jami’in yankin ba.



