Kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen bunkasa harkokin hakar ma’adanai a yankin.
A cewar kungiyar, hakar ma’adanai ya kasance wani jigo ne na bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma rage fatara.
Yayin da yake bayani a wajen wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja, shugaban kungiyar Farfesa Ango Abdullahi, ya koka da cewa an yi watsi da dimbin albarkatun da ke tattare a yankin na arewa, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.



