Kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da na gas (PENGASSAN) ta bayyana cewa babu wata yarjejeniya da suka sa wa hannu kafin janye yajin aikin da suka yi.
PENGASSAN ta janye yajin aikin ne a ranar Laraba bayan shiga da gwamnati ta yi tsakaninta da matatar man Dangote.
Da yake jawabi a wata hira da gidan talabijin na Channels, Shugaban Kungiyar, Featus Osifo ya bayyana cewa takardun da aka gabatar a zaman ba yarjejeniya ba ce don haka ba su rattaba hannu a kai ba saboda suna ganin akwai lauje cikin nadi.
Osifo ya kara jaddada matsayar kungiyar na dole Dangote ya mayar da ma’aikatan da aka dakatar aiki a wurarensu na asali sabanin sauya musu wajen aiki.



