Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya EFCC ta fara binciken wasu fasinjoji biyu da aka kama da kuɗaɗe sama da dala 6,000 da £53,000 a filin jirgin saman Lagos.
Hukumar ta sanar da hakan cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar.
Hukumar ta ce mutanen da ake zargi sun haɗa da Mamud Nasidi da Yahaya Nasidi, kuma jami’an hukumar kula da sufurin jiragen sama FAAN, ne suka kama su.
Rahoton jaridar Punch ya rawaito cewa an kama su ne yayin da suke ƙoƙarin hawa jirgi zuwa Abuja, inda suka ce su jami’an tsaro ne suna tafiya da wani wanda ake zargi.
Bayan kama su, an mika su ga jami’an hukumar DSS kafin daga bisani aka tura su ga EFCC don ci gaba da bincike da yiwuwar gurfanar dasu.



