Ministan Kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin ƙasa, Mr Wale Edun, yana jinya a gidansa da ke Abuja bayan ya kamu da rashin lafiya, kamar yadda majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa suka tabbatar wa jaridar Punch a ranar Lahadi.
Wani babban jami’i a fadar shugaban ƙasa da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa labarin da ke yawo cewa ministan ya kamu da shanyewar baren jiki ko kuma an kai shi ƙasashen waje don jinya ba gaskiya ba ne.
A cewarsa, “Eh, gaskiya yana rashin lafiya, amma ba shanyewar baren jiki ba ne. Yanzu haka yana cikin gidansa, ba a kai shi ko’ina ba.”
Majiyoyin sun kuma tabbatar cewa babu wani shiri daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu na maye gurbin Mr Edun, yayin da ake sa ran lafiyarsa za ta inganta nan ba da jimawa ba.



