Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu matasa biyar bisa zargin gudanar da aure ba tare da amincewar iyaye ba, ciki har da ango da amarya da mutane uku da suka tsaya a matsayin wakilai da shaidu.
Mataimakin kwamandan hukumar, Dr. Mujahideen Aminuddeen, ya ce matasan sun daura auren ne bisa sadaki na Naira Dubu 10 wanda bai kai mafi ƙarancin da Musulunci ya tanada ba, abin da ya sa hukumar ta fara bincike kan lamarin.
Mujahideen ya bayyana cewa, auren ya sabawa ka’idojin Musulunci da na doka, yana mai kira ga iyaye da su kula da harkokin ‘ya’yansu musamman a batun da ya shafi aure.
Lamarin ya faru ne kasa da mako guda bayan gwamnatin Kano ta ba hukumar Hisbah umarnin fara shirin auren gata ga masu bukata fiye da 2,000 a fadin jihar kamar yadda Punch ta ruwaito.



