Ministan kasuwancin jamhuriyar Nijar, Malam Abdoulaye Seydou ya jagoranci kaddamar da sabon ofishin kamfanin shinkafar gida a babban birnin Yamai a ranar Litinin 13 ga watan Oktoba, 2025
Wannan kaddamarwa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin mulkin sojan Nijar ke ikirarin kokarin lalubo hanyoyin samun dogaro da kai a fanni cimaka ga ‘yan kasar