Jigo a jam’iyyar APC daga Jihar Bauchi, Khamis Darazo, ya bayyana cewa ficewar tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, daga jam’iyyar zai kasance babban rashi ga APC musamman a Arewacin Nijeriya.
Darazo ya bayyana haka ne a ranar Lahadi yayin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, inda ya bukaci fadar shugaban kasa da shugabancin jam’iyyar su gaggauta shawo kan lamarin.
A cewarsa, rahotannin da ke cewa Pantami na shirin barin jam’iyyar suna kara tada hankalin magoya baya, yana mai gargadin cewa hakan zai zama babban koma baya ga jam’iyyar a Arewa da ma kasa baki daya.
Punch ta ruwaito cewa, Darazo ya bayyana Pantami a matsayin mutum mai hangen nesa da kwarewa wanda ya sadaukar da kansa wajen yada ilimi, imani da gaskiya wajen inganta mulki da kuma karfafa matasa a fadin Nijeriya.



