Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da nadin Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa majalisar ta amince da nadin Amupitan ne bayan kammala tantanceshi da tare da kada kuri’a da mambobin majalisar suka yi.
Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ne ya jagoranci zaman da aka gudanar a Alhamis dinnan, 16 ga Oktoba, 2025.
Majalisar ta tabbatar da cewa an tantance shi daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin majalisa, da ofishin mai bai wa Tinubu shawara kan harkokin tsaro NSA, da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da cewa ba shi da wani tarihi na laifi.



