Wani lauya kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Liborous Oshoma ya bayyana damuwa kan yawan tafiye-tafiyen da Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ke yi, yana shawartarsa ya rage yawo kasashen waje tare da mai da hankali kan matsalolin tattalin arziki da tsaron Nijeriya.
Rahotanni sun nuna cewa tun bayan rantsar da shi, Shugaba Tinubu ya yi tafiye-tafiye 46 zuwa ƙasashen waje, inda ya zuwa watan Oktoban 2025 ya shafe kwanaki 192 a wajen Nijeriya.
Oshoma, yayin hira da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today, inda ya ce ya dace Tinubu ya yawaita zama a gida domin duba irin matsalolin da ‘yan ƙasa ke fuskanta, maimakon dogaro da bayanan hadimansa.
A cewarsa, da shugaban ƙasa zai tsaya gida na ɗan lokaci ya ziyarci wurare ya ga halin da ake ciki da idonsa, zai fi gane gaskiya fiye da bayanan da ake ba sa.
Ya kuma kara da cewa, yawancin harkokin kasuwanci da tarukan da shugaban na Nijeriya ke halarta a ƙasashen waje za a iya gudanar da su ta intanet domin rage kashe kuɗi, sannan kuma Tinubu na iya tattaunawa da masu zuba jari daga gida, a maida kuɗaɗen da ake kashewa kan tafiye-tafiye zuwa sassan da ke buƙatar tallafi.



