Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta karɓi sabbin mambobi, ciki har da ’yan majalisar wakilai guda biyar da kuma ’yan majalisar dokokin jihar Kaduna huɗu tare da dubban magoya baya.
Wani babban gangami da aka gudanar a ranar Asabar ya sa APC yanzu tana da ’yan majalisar wakilai 13 a jihar ta Kaduna yayin da PDP ta rage da uku.
Haka kuma a majalisar dokokin jihar APC tana da mambobi 26 yayin da PDP ke da guda 8.
Taron, wanda aka gudanar a filin wasa na Murtala Square da ke Kaduna, ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, Ministan muhalli Balarabe Abbas Lawal da shugaban hukumar ci-gaban Arewa maso Yamma Lawal Samaila Yakawada tare da dubban magoya bayan jam’iyyar.
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, yayin da yake jawabi, ya tabbatar wa sabbin shiga cewa APC jam’iyya ce ta haɗin kai wadda ba ta nuna bambanci tsakanin sabbi da tsofaffin mambobinta, yana mai cewa duk wanda ya shigo jam’iyyar APC a yau da waɗanda suka dade a ciki suna da dama iri guda.



