Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ya sanya hannu kan dokar kirkirar sabbin masarautu 13 a fadin jihar.
Daily Trust ta ruwaito cewa a lokacin da yake sanya hannu kan dokar, gwamnan ya yi gargadi kan siyasantar da kowane bangare na sabbin masarautun, tare da bukatar a mutunta doka.
Ya kuma ce duk wanda aka samu da saba ka’ida ko taka doka zai fuskanci hukunci.