Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta bayyana karbar ‘yan kasar 147 da suka makale a Libya.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta bayyana cewa dawo da ‘yan kasar wani bangare ne na shirin mayar da mutane ainahin kasashensu, na hadin gwiwa tsakanin majalisar dinkin duniya da kuma gwamnati.
Labari mai alaka: Hukumomi a Nijeriya sun karbi ‘yan kasar 139 daga jamhuriyar Nijar
Mutanen da hukumar ta karba sun hadar da manyan maza da mata guda 100, sai yara maza da mata 34, sannan jarirai guda 13.
Tuni dai NEMA ta bayyana cewa an fara shirin daukar bayanan su ta hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya, kafin mayar da su cikin al’umma.



