Sanata Muntari Dandutse mai wakiltar Katsina ta Kudu a jam’iyyar APC ya bayyana sauya sheka daga jam’iyya zuwa wata a matsayin cin amanar jama’ar da suka ba da kuri’unsu.
Yayin muhawarar da majalisar dattawa ta yi kan kudirin sauya dokar zaɓe a ranar Laraba, Dandutse ya ce ya zama dole a samar da doka mai tsauri da za ta takaita yin hakan, inda ya ce ba za ka iya lashe zaɓe a jam’iyya guda sannan ka canza sheka ba tare da doka mai tsauri ba, domin hakan na tauye amanar da jama’a suka ba ka.
Sanatan ya ƙara da cewa duk wani gyara da za a yi wa dokar zaɓe dole ne ta mayar da hankali wajen dawo da amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyya da tabbatar da mutuncin zaɓe a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa, Dandutse ya kuma jaddada bukatar gudanar da dukkan zaɓe a rana ɗaya da bai wa hukumar zaɓe ta INEC ikon gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi domin inganta tsarin mulki.
Sanatan shi ne ɗan majalisar farko daga jam’iyyar mai mulki da ya fito fili ya soki sauye-sauyen jam’iyya da ‘yan majalisun ke yi zuwa cikin jam’iyya mai mulki.