Wata ƙungiya mai goyon bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu a jam’iyyar APC, mai suna Renewed Hope Advocates for Tinubu 2027, ta gargadi shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan matakan da ake zargin yana ɗauka domin hana Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, shiga jam’iyyar.
A wata sanarwa da kodinetan kungiyar na ƙasa, Kwamared Zakari Mohammed, ya fitar ya ce irin waɗannan matakai na iya lalata yunƙurin sasanci da shugaba Tinubu ke jagoranta, da kuma ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa APC gabanin zaɓen 2027.
Rahotanni sun nuna cewa shugabannin APC na Filato ƙarƙashin jagorancin Farfesa Yilwatda sun amince da wani kuduri da zai hana gwamnan shiga jam’iyyar duk da cewa Mutfwang ya musanta niyyar canza sheƙa. Kungiyar ta ce abokan Tinubu na ci-gaba da tuntuɓar manyan ‘yan adawa domin ƙara faɗaɗa jam’iyyar a matsayin shirin haɗin kan ƙasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa halayen irin waɗannan shugabanni ba su dace da tsarin shugabanci mai haɗin kai da Shugaba Tinubu ke gina wa ba, wanda manufarsa ita ce kafa jam’iyya ɗaya mai ƙarfi da haɗin kai fiye da bambance-bambancen siyasa.



