DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sabon shugaban hukumar zaben ya yi alwashin dawo da ingantacce da sahihin zabe a Nijeriya

-

Sabon shugaban hukumar zaɓen Nijeriya, INEC, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya sha alwashin dawo da sahihanci da amincewar jama’a ga tsarin zaɓe na ƙasar, yana mai cewa nadin da aka yi masa kiran Allah ne don ya yi wa ƙasa hidima.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, yayin jawabinsa bayan rantsuwar kama aiki da shugaban ƙasa ya yi masa a fadarsa daga ke Abuja a ranar Alhamis, Amupitan ya ce manufarsa ita ce tabbatar da zaɓe mai ‘yanci, adalci da gaskiya, tare da ƙarfafa darajar dimokuraɗiyya a duk faɗin ƙasa.

Google search engine

Farfesan ya ce, zaɓen gwamnan Jihar Anambra da ke tafe zai zama muhimmin gwaji ga hukumar, yana mai jaddada cewa nasarar INEC za ta dogara ne kan haɗin kai, ladabi da gaskiya a tsakanin ma’aikata. Ya kuma yi alkawarin kiyaye gaskiya da bayyana komai a ayyukan hukumar, tare da kula da walwalar ma’aikata domin tabbatar da ingantaccen zaɓe.

Amupitan ya ƙara da cewa, idan har muna so mu dawo da sahihin zaɓe, dole mu tabbatar da cewa kowanne ɗan Nijeriya yana da tabbacin cewa kuri’arsa za ta ƙirgu, domin hakan ne ke gina amincewa da tsarin dimokuraɗiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Hukumar Tarayyar Turai ta yi Allah-wadai da haramta biza da Amurka ta yi wa wasu Turawa

Tarayyar Turai, tare da ƙasashen Faransa da Jamus, sun yi kakkausar suka ga matakin Amurka na haramta biza ga wasu ’yan Turai da ke yaki...

Shugaba Tinubu ya yi kira ga hadin kai da hakuri a tsakanin addinai a cikin sakon taya murnar bikin Kirsimeti

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su rungumi haɗin kai, juriya da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, yana mai cewa...

Mafi Shahara