Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya naɗa yayansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sarkin sabon masarautar Duguri da aka ƙirƙira a jihar.
Sakataren gwamnatin Jiha, Aminu Hammayo ne ya mika wa sabon sarkin takardar naɗin a madadin gwamnan yayin wani biki da aka gudanar a fadar sarkin da ke Duguri, cikin ƙaramar hukumar Alkaleri, a ranar Juma’a.
A yayin taron, sakataren gwamnatin ya ja hankalin sabon sarkin da ya cigaba da mara wa gwamnati baya wajen aiwatar da manufofinta domin ci-gaban al’umma.
Da yake jawabi, sabon sarkin Duguri ya gode wa gwamnan jihar, Bala Mohammed bisa wannan gagarumar dama, tare da yin addu’ar Allah Ya saka masa da alheri kuma ya yi alkawarin yin biyayya ga gwamnatin da kuma majalisar masarautar jihar.



