Ƙungiyar Shugabannin Jam’iyyar ADC a Jihohin Najeriya ta sake tabbatar da Engr. Bala Sufiyanu a matsayin sahihin shugaban jam’iyyar na jihar Kebbi, daidai lokacin da wani bangare na jam’iyyar ya sake jaddada goyon bayansa ga Dr. Sule-Iko a matsayin shugaban jam’iyyar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa ga manema labarai da Ƙungiyar Shugabannin Jihohin ADC ta fitar a ranar Lahadi, 26 ga Oktoba 2025, mai ɗauke da sa hannun Shugaban ƙungiyar, kuma Shugaban ADC na Jihar Kogi, Hon. Kingsley T. Ogga.
Ƙungiyar ta zargi Dr. Sule-Iko da naɗa kansa bisa son rai a matsayin shugaban ADC na Jihar Kebbi, ta kuma bayyana hakan a matsayin matakin da bai dace ba, inda ta ce hakan karya tsarin jam’iyyar ne da yunƙurin haifar da rikici.
A cewar wani ɓangare na sanarwar:
“Ƙungiyar Shugabannin ADC a jihohi ta yi watsi da ikirarin Dr. Sule-Iko, saboda ya keɓe kansa daga tsarin jam’iyya. Engr. Bala Sufiyanu shi ne sahihin shugaban ADC a Kebbi bisa amincewar kwmaitin NEC na jam’iyyarmu”
Sai dai kuma a wani martani daga wani tsagi na jam’iyyar ADC a Jihar Kebbi, bangaren ya yi watsi da wannan matsaya, yana mai cewa an tauye wa Dr. Sule-Iko hakkinsa.
A wata sanarwa ta daban da DCL Hausa ta samu, bangaren da ke goyon bayan Dr. Sule-Iko ya bayyana cewa:
“Dakatar da Dr. Sule-Iko bai bi matakan doka ba, don haka shi ne har yanzu shugaban ADC na gaskiya a Jihar Kebbi.”
A halin da ake ciki, Ƙungiyar Shugabannin ADC na Jihohi ta umarci Engr. Bala Sufiyanu da ya kafa kwamitin ladabtarwa mai mutum biyar don gayyatar Dr. Sule-Iko ya yi bayani kan zargin rashin bin tsarin jam’iyyar da ake masa tare da ba shi damar kare kansa.



