Ina matukar tausayin mazaje masu mata daya, akwai nutsuwa tattare da auren mace fiye da daya, in ji wani Sanata daga kudancin Nijeriya
Sanata Ned Nwoko ya ce yana tausayin maza masu mata ɗaya, yana mai jaddada cewa auren mace fiye da ɗaya na kawo daidaito da kwanciyar hankali ga maza.
Dan majalisar da ke wakiltar Delta North ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa a shirin Politics Today na tashar Channels Television.
Nwoko, wanda ke da mata huɗu, ya ce bai taɓa nadamar zaɓin sa na aure ba.
Ya kuma karyata jita-jitar da ke cewa yana cin zarafin ɗaya daga cikin matansa, jarumar fina-finan Nollywood, Regina Daniels.



