Gwamnatin jihar Bauchi ta mika bukatar neman a bata damar kirkirar sabbin kananan hukumomi 29 a jihar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa mataimakin magatakardar Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Musa Yerima, ne ya aika da bukatar neman sahalewar kwamitin gyaran kundin tsarin mulki na kasa domin amincewa.
A halin yanzu, Bauchi na da kananan hukumomi 20 da kundin tsarin mulki na 1999 ya amince da su,idan aka ƙara waɗannan sabbin guda 29 da ake nema, yawan kananan hukumomin jihar zai kai 49,wadda ke da kusan al’umma miliyan 10.
A cikin wasikar da Yerima ya aika wa shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan gyaran kundin tsarin mulki, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa suna neman sabbin kananan hukumomin ne bisa tanadin Sashe na 100, sakin layi na 3 na kundin tsarin mulki, kuma ana neman sahalewar Majalisun kasar ta amince da su bisa Sashe na 8(5).



