DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamna Abba Gida Gida ya zabi tsohon shugaban ma’aikatansa da wasu mutum 5 a matsayin kwamishinoni

-

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya tura sunayen mutane 5 zuwa ga majalisar dokokin jihar domin ta tantancesu a matsayin kwamishinoni.
Kakakin majalisar dokokin jihar Isma’il Jibrin Falgore ne ya karanta wasikar gwamnan a zaman majalisar na yau Litinin, a cewar jaridar Dailytrust.
Mutanen da gwamnan ke son majalisa ta tantance sun hada da tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatinsa, Shehu Sagagi, da Dr Dahiru Mohd Hashim, da Ibrahim Abdullahi Wayya, da Dr Isma’il Dan Maraya, da Gaddafi Sani Shehu da kuma Abdulkadir AbdulSalam.
Wannan na zuwa ne, kwanaki kadan bayan da gwamnan ya kori sakataren gwamnati Abdullahi Bichi, tare da wasu kwamishinoni 5 tare da roshe ofishin shugaban ma’aikata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da ziyarar ibada ta Kiristoci zuwa Isra’ila

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da duk wata ziyara ta Kirista zuwa Isra’ila sakamakon halin tsaro a Gabas ta Tsakiya. Hukumar kula da ziyarar ibada...

Mata biyu da ke tsare a hannun ‘yan bindiga sun haihu a jihar Sokoto

Wasu mata biyu cikin mutum takwas da aka sace a kauyen Takatsaba da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto sun haifi jarirai namiji...

Mafi Shahara