Jam’iyyar PDP ta sake fadawa cikin rikici yayin da sabuwar rarrabuwar kai ta kunno kai a cikin shugabancinta, inda wani bangare mai goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, ya sanar da dakatar da mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Umar Damagum, da wasu mambobin kwamitin gudanarwa guda biyar.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Asabar a madadin bangaren, sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya bayyana mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa ta Tsakiya, Mohammed Abdulrahman, a matsayin sabon mukaddashin shugaban jam’iyyar.
Anyanwu ya ce an dakatar da Damagum bisa rashin iya aiki, almundahana, da kin bin hukuncin kotu, tare da tura shi gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.
Haka kuma ya kara da cewa an dakatar da mai magana da yawun jam’iyyar, Debo Ologunagba, bisa fitar da sanarwa ba tare da izini ba, sai mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin kudu, Taofeek Arapaja, da kuma mai kula da harkokin kudi, Daniel Woyenguikoro, bisa zargin almundahana.
Hakazalika, an dakatar da shugaban matasa na kasa, Sulaiman Kadade, da mataimakin sakataren kasa, Setonji Koshoedo, na tsawon kwanaki 30 kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sai dai a baya, kwamitin karkashin jagorancin Damagum shi ma ya dakatar da Sanata Samuel Anyanwu, lauyan jam’iyyar, Kamaldeen Ajibade (SAN), da wasu mambobi biyu, abin da ya kara tsananta rikicin cikin gida da jam’iyyar ke ciki a halin yanzu.



