Kungiyar shugabannin jam’iyyar SDP na jihohi 37 ta tabbatar da cewa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, har yanzu yana cikin dakatarwa daga jam’iyyar na tsawon shekaru 30.
Wannan sanarwa ta fito ne bayan jita-jitar da ke yawo cewa El-Rufai na shirin komawa cikin jam’iyyar kafin babban taronta na kasa.
Shugaban kungiyar, Femi Olaniyi, ya shaida wa jaridar PUNCH a ranar Lahadi an Abuja cewa, babu komawa baya a kan hukuncin da kwamitin gudanarwa na kasa ya dauka kan El-Rufai.
A cewarsa, El-Rufai ya shiga jam’iyyar ne ta bayan gida kuma tun a ranar 3 ga watan Afrilu, 2025 an bayyana cewa duk wanda ke son shiga jam’iyyar sai ya bi matakin ofishin mazaba da na jiha, amma El-Rufai bai bi wannan hanya ba. Don haka ne kwamitin kasa ya dakatar da shi har na shekaru 30, kuma wannan hukunci ba zai canza ba.



