Da yiyuwar kara samun rikici a jam’iyyar PDP yayin da bangarorin shugaban jam’iyya Umar Damagum da sakatare Samuel Anyanwu ke shirin komawa aiki a ofishin jam’iyyar na kasa da ke Wadata Plaza, Abuja, a yau Litinin.
A ranar Asabar, bangaren Damagum ya gudanar da taro a Legacy House da ke Maitama, yayin da bangaren Anyanwu kuma ya yi nasa taron a ofishinsa da ke Wuye a Abuja.
Wata majiya daga jam’iyyar ta shaida wa Daily Trust cewa duka bangarorin biyu na shirin yin aiki a ofishin jam’iyyar guda, abin da ke haifar da fargaba a tsakanin ma’aikata na jam’iyyar.
Majiyar ta kara da cewa bangaren Nyesom Wike na kokarin jan hankalin wasu mambobin kwamitin gudanarwa domin samun rinjaye a cikin jam’iyyar, lamarin da zai iya haddasa sabon rikici idan duka bangarorin suka hadu a ofishin a yau.



