Wasu magoya bayan bangaren sabon mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP, Mohammed Abdulrahman, sun mamaye hedkwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja, a ranar Litinin suna rera wakokin goyon baya, tare da bukatar bangaren Umar Damagum ya bar ofis nan take.
Rahotanni sun ce rikicin cikin gida na jam’iyyar ya kara kamari bayan dakatar da sakataren jam’iyya, Sanata Samuel Anyanwu, da lauya Kamaldeen Ajibade na tsawon wata guda, abin da ya haifar da kafa sabon bangare karkashin Abdulrahman.
A daya bangaren, magoya bayan ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, sun gudanar da taro a wani wuri daban inda suka sanar da dakatar da Damagum da kwamitinsa.
Jami’an tsaro sun bazu a wurin domin hana tashin hankali yayin da bangarorin biyu ke kokarin kwace ikon ginin jam’iyyar, inda bangaren Abdulrahman ya mamaye ofishin shugaban jam’iyya na kasa.



