Dan wasan baya na Arsenal, William Saliba, ya bayyana cewa sha’awar da Real Madrid ta nuna masa na da matukar daukar hankali, amma burinsa shi ne ya lashe kofuna tare da Arsenal kafin tunanin komawa wata kungiya.
A wata tattaunawa da gidan talabijin na Telefoot, Saliba ya ce, hakika yana da daukar hankali idan kulob kamar Real Madrid ta nuna sha’awa a kanka, amma yana so ya fara lashe kofuna da Arsenal kafin yin tunanin wani abu dabam.
Saliba, dan shekara 22, ya kasance ginshikin tsaron Arsenal tun bayan dawowarsa, inda ya taimaka wa kungiya ta fafata a manyan gasanni.
Wannan furuci nasa na nuni da cewa har yanzu yana da cikakken jajircewa ga Arsenal duk da rade-radin da ke danganta shi da Real Madrid da sauran manyan kungiyoyi.



