Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC a hukumance a wani biki da aka gudanar a filin wasa na Samson Siasia da ke Yenagoa a ranar Litinin.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya jagoranci tawagar manyan jiga-jigan APC ciki har da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da wasu gwamnoni.
Diri, wanda ya yi murabus daga PDP a watan Oktoba, ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa APC ne don ceto jihar Bayelsa daga halakar PDP wadda ya kira da jirgin da ke nitsewa kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Haka kuma ya kara da cewa, sauyawar tasa ba ta mutum daya ba bace, ta al’ummar Ijaw ce baki daya kuma yana yaba wa shugaba Tinubu bisa aiwatar da aikin hanya daga Legas zuwa Kalaba wadda ya ce soyayya ce ga mutanen Ijaw.



