Babbar kotun jihar Oyo da ke Ibadan ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a A. L. Akintola, ta bai wa jam’iyyar PDP damar gudanar da babban taronta na kasa da aka shirya yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamban 2025, a filin wasan Lekan Salami da ke Ibadan.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da wani ɗan takara, Folahan Malamo Adelabi, ya shigar a kotu yana neman a tabbatar da bin jadawalin da jam’iyyar ta fitar tare da hana PDP da jami’anta yin wani abu da zai iya katsewa ko hana taron.
Mai shari’a Akintola ya kuma umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC, da ta tura masu bibiya don tabbatar da gaskiya da bin doka a taron.
Hukuncin ya bai wa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, wanda shi ne shugaban kwamitin shirya taron damar kammala shirye-shiryen da suka hada da halartar wakilai fiye da 3,000 daga fadin kasar.



