DCL Hausa Radio
Kaitsaye

’Yan Majalisar Amurka 9 sun bukaci Amurka ta dauki mataki kan rikicin zaben Kamaru

-

Wasu ’yan majalisar dokokin Amurka tara sun rubuta wa sakataren harkokin wajen kasar, Marco Rubio, suna nuna damuwa kan tashin hankali, kisa, da kama mutane da dama da suka biyo bayan zaben shugaban kasa na Kamaru da aka gudanar a ranar 12 ga watan Oktoba.

A cikin wasikar, ’yan majalisar sun soki yadda gwamnati ke danniya kan masu zanga-zanga cikin lumana, tare da kira da a hukunta wadanda ke da hannu wajen kashe fararen hula. Sun bukaci gwamnatin Amurka ta matsa wa hukumomin Kamaru lamba domin su mutunta dimokuradiyya da hakkin dan Adam.

Google search engine

Wannan mataki ya biyo bayan yadda ake samun matsin lamba daga kasashen duniya, bayan rahotannin kashe mutane da dama da kama daruruwan mutane da kuma takurawa ’yan adawa bayan sake zaben shugaba Paul Biya da ake tantama a kai.

Masana harkokin diflomasiyya na ganin wannan matakin na ’yan majalisar Amurka a matsayin alamar cewa Washington na bin lamarin Kamaru da ido sosai kamar yadda jaridar MMI News ta wallafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Akwai yiwuwar madugun adawar Kamaru Isa Tchiroma yana Nijeriya ya boye – Rahotanni

Madugun adawar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, wanda ya kalubalanci nasarar Paul Biya, yana iya kasancewa yana a Nijeriya kamar yadda Africa Intelligence ta ce, amma...

Fusatattun matasa sun hallaka limamin masallaci a jihar Kwara bisa zargin maita

Wasu fusatattun matasa a garin Sokupkpan da ke ƙaramar hukumar Edu a jihar Kwara sun hallaka limamin masallacin yankin, Malam Abdullahi Audu, bisa zargin cewa...

Mafi Shahara