Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya gargadi wanda aka zaba domin mukamin minista, Barista Kingsley Udeh (SAN), da kada ya amsa kowace tambaya da ta shafi kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da Nijeriya.
Udeh, wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zaba domin maye gurbin tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya bayyana a gaban majalisar a ranar Alhamis don tantancewa.
Nnaji ya yi murabus ne a watan da ya gabata bayan cece-kuce kan sahihancin takardun karatunsa.
Lokacin tantancewar, Akpabio ya bukaci Udeh da ya gabatar da kansa sannan ya ce, tambayar da kawai zan roƙe ka kada ka amsa ita ce wadda ta shafi Trump.
Daga karshe, majalisar ta amince da nadin Udeh a matsayin minista ta hanyar kada kuri’ar murya.



