Majalisar dokoki ta Amurka ta gabatar da sabon kudiri mai taken “Nigeria Religious Freedom Accountability Act of 2025”, wadda ke neman hukunta jami’an gwamnatin Nijeriya da ake zargin suna da hannu wajen take hakkin ’yancin addini da cin zarafin jama’a.
Kudirin, wanda dan majalisa Marlin Stutzman daga jihar Indiana ya dauki nauyinsa, an gabatar da shi ne a ranar 21 ga Oktoba, kuma yanzu yana gaban kwamitocin kula da harkokin wajen Amurka da na shari’a domin nazari.
A cikin kudirin, an umarci shugaban Amurka da ya sanya takunkumi ga jami’an Nijeriya da ke da hannu ko suka amince da cin zarafi na addini, ciki har da gwamnoni, alkalai, da jami’an tsaro da suka aiwatar da dokokin batanci ko suka rufe ido kan tashin hankali da aka yi da sunan addini.
Idan aka amince da kudirin, zai bai wa Amurka damar sanya takunkumi kan duk wani jami’i ko hukumomi a Nijeriya da ake zargin suna goyon bayan zalunci ko laifukan da suka saba wa ’yancin addini, abin da zai kara tsananta matsin lamba daga Washington kan Nijeriya.



