Wasu fusatattun matasa a garin Sokupkpan da ke ƙaramar hukumar Edu a jihar Kwara sun hallaka limamin masallacin yankin, Malam Abdullahi Audu, bisa zargin cewa shi ne ya haddasa mutuwar wani mazaunin garin mai suna Ibrahim Gana ta hanyar maita.
Shaidu sun ce lamarin da ya faru a ranar Laraba inda ya jefa al’umma cikin firgici da tashin hankali. Gana, wanda ya rasu yana fama da rashin lafiya, ya sha cewa limamin ne ke damunsa a mafarki, abin da ya sa wasu suka fara yarda cewa yana da hannu cikin ciwonsa.
A cewar majiyoyi, bayan rasuwar Gana, ’yan’uwansa suka tattara wasu matasa suka kai wa limamin hari, duk da ƙoƙarin dattawa na hana su. Sun bugi malamin har lahira suna zargin ya kashe Gana ta hanyar maita.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kakakin ’yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar al’amarin, tana mai bayyana shi da mummunan al’amari.



