Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da ceto mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Honarabul Samaila Muhammad Bagudu, daga hannun ‘yan bindiga bayan wani samame da jami’an tsaro suka gudanar.
A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Yakubu B. Tafida, ya fitar ranar Asabar, gwamnati ta bayyana cewa an ceto dan majalisar lafiya lau, kuma yana karɓar kulawar da ta dace daga hukumomin lafiya.
DCL Hausa ta ruwaito cewa, gwamnatin ta yaba ƙoƙarin hadin gwiwar jami’an tsaro da suka jagoranci aikin ceton.
Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa gwamnatin Kebbi ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin kawar da matsalar ‘yan bindiga da sauran barazanar tsaro a jihar.
Gwamnati ta roƙi jama’a su ci gaba da goyon bayan hukumomin tsaro tare da kasancewa masu lura da abin da ke faruwa a yankunansu, da kuma sanar da hukumomi duk wata alama ta abin da ake zargi.



