Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya gargadi manoma da makiyaya da ke rikici a karamar hukumar Arewa ta jihar su daina fada su zauna lafiya, inda ya ce duk wanda aka kama yana tayar da fitina za a kama shi a gurfanar da shi gaban kotu.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga mutanen da suka rasa matsuguni sakamakon rikicin, wadanda ke samun mafaka a ofishin karamar hukumar da ke Kangiwa.
A cewarsa, yaje ne don jajanta wa iyalan wadanda suka mutu a wannan mummunan rikici, sai dai ya gargadi garesu da su daina daukar doka a hannu.
Gwamnan ya kuma ce ana nan ana gudanar da bincike,duk wanda aka kama da hannu kan wannan rikici tabbas zai fuskanci fushin hukuma tare da gurfanar da shi domin daukar mataki na gaba.



