DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Atiku da Kwankwaso ba za su taba zama inuwar jam’iyya guda ba – Jigo a APC

-

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kudu maso gabashin Nijeriya Ijeoma Arodiogbu, ya ce rade-radin da ake yi cewa Atiku Abubakar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin yin kawance kafin zaben 2027 ba shi da tushe ballantana makama.

Jaridar Punch ta rawaito Arodiogbu na cewa babu wata hanya da tsohon gwamnan na Kano zai koma tafiya ɗaya da Atiku, duk da kyakkyawar mu’amalar da suka nuna a bikin zagayowar ranar haihuwar Kwankwaso makonni biyu da suka gabata.

Google search engine

Ya ce idan Kwankwaso zai yi wani sauyi, zai fi dacewa ya koma APC domin hakan zai fi amfani a siyasarsa, ya ce ko da Atiku ya yi yunƙurin bai wa Kwankwaso wata dama hakan ba zai yi wani tasiri ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kungiyar MPLJ a Nijar ta dau alhakin hari kan bututun man Nijar a yankin Agadem

Kungiyar 'yan tawaye ta' Mouvement Patriotique pour la Liberté et la Justice' wato MPLJ ta dauki alhakin harin da aka kai a wannan rana ta...

Ina sharbar hawaye a duk lokacin da na samu labarin halaka mutane – Godswill Akphabio

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Godswill Akpabio, ya ce gwamnati na da nauyin dawo da zaman lafiya a jihar Filato da Nijeriya baki ɗaya a...

Mafi Shahara