Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kammala aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta mai zaman kanta, kamar yadda Kwamishinan Makamashi, Alhaji Sanusi Danfulani, ya bayyana yayin ziyarar duba aikin da aka kai ranar Laraba.
Kamar yadda Kwamishinan ya shaida wa manema labarai, gwamnatin jihar ta zuba biliyoyin naira a aikin, tare da ƙarin N1.5bn da Gwamna Ahmad Aliyu ya saki kwanan nan domin gyare-gyare da kammala aikin.
A yayin da yake karin haske, Daraktan Sashen Lantarki na ma’aikatar, Injiniya Abubakar Shehu, ya bayyana cewa an gwada wasu sassan injinan a makon da ya gabata, sai dai ya ƙi fayyace matakin da gwamnati za ta ɗauka kan yadda za a tura wutar zuwa jama’a, yana mai cewa wannan ya rage ga hukumomin wutar lantarki.
Rahotanni sun nuna cewa aikin na megawatt 38 an bai wa kamfanin Vulcan Capital Energy na Amurka ne a 2008 kan kuɗin N3.8bn da wa’adin watanni shida, amma an yi ta tsawaita lokacin kammalawa daga 2009 zuwa 2010, 2011, 2013, 2014, 2016 har zuwa 2019 kafin a ce yanzu an kammala shi.



