Gwamnatin jihar Kebbi ta bukaci al’umma su tsananta addu’o’i domin ceto ɗaliban GGCSS Maga da ’yan ta’adda suka sace, kamar yadda kwamishinan harkokin addini, Sani Aliyu, ya bayyana a Birnin Kebbi.
jaridar Punch ta ruwaito kwamishinan ya ce halin da ake ciki ya zarce ƙarfin ɗan adam, don haka ana buƙatar cikakken taimakon Allah duk da ƙoƙarin gwamnati da jami’an tsaro.
Aliyu ya roƙi malamai, limamai, da masu ibada su rika yin qunut da addu’o’i a cikin sallolinsu, musamman a cikin dare. Haka kuma ya bukaci fastoci da su ware lokuta a cikin wa’azozinsu da taron ibada domin roƙon zaman lafiya a Kebbi da Nijeriya gaba ɗaya.
Hakazalika, kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’a su kasance masu lura, su nisanci hulɗa da miyagu, tare da tura duk wani muhimmin bayani ga jami’an tsaro domin taimakawa wajen gano masu laifi da kuma ceto ɗaliban cikin gaggawa.



