Shugaban Amurka Donald Trump ya sake sukar Nijeriya, inda ya kira ta da “abin kunya” tare da zargin gwamnati da kasa dakile kashe-kashen da ake yi wa ’yan ƙasa. Ya ce ana kashe mutane dubbai ba tare da wani mataki ba, inda ya zargi gwamnati da gazawa.
Kalaman Trump sun zo ne bayan ya sake saka Nijeriya a jerin ƙasashen da ake kula da su na musamman, yayin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta tura mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, zuwa Amurka don gabatar da bayanai kan matakan tsaro.
Tun bayan kalaman Trump, hare-haren sun ƙaru a yankuna daban-daban inda ‘yan bindiga suka halaka babban hafsan soja a Borno, yayin da barayin daji suka sace dalibai mata 25 a Kebbi tare da halaka mataimakin shugaban makarantar.
A ciki ƙarin hare-haren, ’yan bindiga sun kutsa coci a Eruku, Kwara, sannan suka sace fiye da ɗalibai 300 da malamai 12 daga makarantar St Mary’s a Papiri, Jihar Neja, abin da ya kara nuna tsananin tabarbarewar tsaro a ƙasar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.



