Fira-ministar kasar Italiya, Giorgia Meloni, ta bukaci gwamnatin Nijeriya ta kara tsaurara matakan tsaro domin kare Kiristoci a sassa daban-daban na Nijeriya.
A wata sanarwa da ta wallafa a X a ranar Juma’a, Meloni ta bayyana harin da aka kai wa al’ummomin Kirista a Nijeriya a matsayin mummuna kuma abin ƙyama. Ta bukaci hukumomi su dauki matakin gaggawa domin hukunta masu aikata irin wadannan laifuka.
Jaridar Punch ta ruwaito Meloni ta ce ’yancin yin addini hakki ne da ba ya karyewa, tana mai jaddada cewa dole ne gwamnati ta kare dukkan rukunan addinai ba tare da wariya ba.
Haka kuma ta nuna alhini ga iyalan da lamarin ya shafa da al’ummomin da ke fargaba sakamakon hare-haren da ake kai musu.
Wannan furuci ya fito ne a lokacin da ake cikin damuwa kan yadda hare-haren ’yan bindiga, ’yan ta’adda ke kamari kan al’umma a Nijeriya, tare da sace-sace da kai farmaki ga kauyuka.



