Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin, ya ce Arewa na da duk abin da ake bukata domin shawo kan matsalar tsaro idan shugabanni da muhimman cibiyoyi suka tashi tsaye tare da aiki da juna.
Barau ya bayyana haka ne a bikin cika shekaru 25 da kafa kungiyar tuntuba ta Arewacin Nijeriya, ACF da aka yi a Kaduna kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A cewarsa, Arewa na da ƙarfi, jagoranci da albarkatun da za su magance matsalolin tsaro, yana mai cewa haɗin kai da tsari guda ne kawai ake bukata domin maimaita nasarorin da aka samu a wasu yankuna na ƙasar kuma babu abin da zai hana Arewa ta yi hakan idan aka daidaita matsayi.
Sanata Barau, wanda ya wakilci shugaban majalisar dattawa, ya taya ACF murnar cikarta shekaru 25, yana yaba wa rawar da ta taka wajen kare muradun Arewa da tallafawa ci-gaban ƙasa. Ya kuma tuna da jajircewar dattawan da suka kafa kungiyar, wasu daga cikinsu a yanzu sun rasu.
Hakazalika ya kara da cewa rahoton da jagorancin ACF ya gabatar kan karuwar rashin tsaro da gibin ci gaba bai kamata ya rufe tarihin juriyar Arewa ba, wadda ta dade tana nuna ƙarfin hali da haɗin kai a lokutan ƙalubale.



