Sojojin birget na 6 na rundunar sojin Nijeriya sun kama wani da ake zargi da satar mutane mai suna Umar Musa Geyi, a Wukari da ke jihar Taraba a ranar 22 ga watan Nuwamba 2025, yayin da ake zargin yana neman kudin fansa na Naira miliyan 20 daga iyalan wanda aka sace.
Ana zargin wanda aka kama yana da hannu a sace Alhaji Jano, wani Bafulatani mazaunin Jandei–Kulala, wanda aka sace a ranar 13 ga watan Nuwamba, kuma har yanzu yana hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.
Kwamandan birget na 6, Birgediya-Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa sojojin kan kwarewarsu, inda ya jaddada kudurin rundunar na karyawa da kawar da dukkan hanyoyin aikata laifuka a jihar.



