Kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC a Yankin Arewa ta Tsakiyar Nijeriya ta bayyana nadamarta bayan ta dage kai da fata sai an naɗa dan yankin a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.
An dai ware kujerar shugaban APC na ƙasa ga Arewa ta Tsakiyar Nijeriya a taron jam’iyyar na 2022, abin da ya haifar da fitowar tsohon Gwamnan Nasarawa, Adamu Abdullahi. Amma bayan murabus ɗinsa a 2023 ba tare da kammala wa’adin ba, sai aka naɗa Abdullahi Ganduje, tsohon Gwamnan Kano daga Arewa maso Yamma, a matsayin shugaban jam’iyyar.
Kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC a Arewa ta Tsakiyar Nijeriya wadda ta ƙunshi manyan jiga-jigan jam’iyyar daga jihohin yankin, ta yi zanga-zanga, tarurruka, taron manema labarai da bayanai domin ganin an mayar da kujerar ga yankin. A ƙarshe, a ranar 24 ga Yuli, 2025, aka naɗa Farfesa Nentawe Yilwatda daga Jihar Filato a matsayin shugaban jam’iyyar.
Sai dai yanzu kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC Forum ta ce Yilwatda ya gaza nuna ƙwarewar jagoranci.
Kungiyar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da Shugabanta, Alhaji Saleh Zazzaga, ya fitar a Abuja.



