Shugaba Tinubu ya tura sunayen mutane uku ga majalisar dattawa domin tantancewa a matsayin jakadu na Nijeriya a wasu kasashen waje.
Shugaban majalisar dattawan Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar a zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya bayyana cewa jerin sunayen farko ya kunshi mutum uku ne kawai.
A cewar Akpabio, sunayen da shugaban kasa ya aika sun hada da Kayode Are daga jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga jihar Jigawa sai Ayodele Oke daga jihar Oyo.
Wannan matakin dai na zuwa ne yayin da gwamnati ke ci gaba da cike guraben diflomasiyya da suka yi saura tun bayan rushe sunayen wadancan jakadu a farkon mulkin Tinubu.



