Wani bincike da jaridar Punch ta ruwaito ya nuna jihohi 14 na Arewacin Nijeriya sun karbi Naira Biliyan 56 domin inganta tsaro a cikin watanni tara na 2025, duk da cewa hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane sun ƙara tsananta a jihohin Neja, Kebbi, Kano da Kwara.
Daga cikin manya-manyan hare-haren akwai sace dalibai 315 da malamai 13 a Papiri, tare da ƙarin mutane 26 a Kebbi da 24 a Shiroro.
Yawaitar hare-haren ya tayar da hankulan jama’a, musamman bayan an sake yin garkuwa da mata masu juna biyu, yara da masu shayarwa a Kwara da Kano cikin mako guda. Lamarin da ya tilasta shugaba Tinubu ayyana dokar gaggawa kan tsaro tare da umartar daukar karin jami’an tsaro 20,000.
Duk da cewa kuɗin inganta tsaro na nufin daukar matakan gaggawa da tattara bayanan sirri, jama’a na zargin ana batar da kudaden ne kawai ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba.
Binciken ya nuna jihohin sun kashe kusan rabin Naira Biliyan 101 da suka ware a 2025, amma hare-hare na ci-gaba da yi wa Arewa barazana.



