DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Najeriya ta kwaso yan kasar Kusan 200 da aka kulle a gidan yarin Libya

-

Gwamnatin Najeriya
ta kwaso yan asalin kasar 161 da aka daure su a gidajen yarin kasar Libya daban-daban
sakamakon aikata laifukan da suka sabawa ka’idar yin kaura.

Jakadan Najeriya a Libya Ambasada Kabiru Musa ne ya bayyana hakan a wata
sanarwa da ya fitar ga manema labarai a birnin tarayyar kasar Abuja.

A cewar Ambasada Musa gwamnatin Najeriya
ta rika kai gwauro da kai mari wajen ganin an saki mutanen da aka garkame a
gidan yarin don basu damar komawa gida, da nufin sake gina rayuwar su.

Sanarwar ta kuma kara da cewa tuni
mutanen suka isa Najeriyar, yayin da aka gargade su da su kaucewa yunkurin tsallakawa
zuwa turai ta barauniyar hanya don gudun fadawa hannun hukumomi ko kuma bata
gari.

Wannan dai ba shine karon farko da ake samun ‘yan Najeriya da dama na
tsallakawa zuwa turai da saharar Libya ba, inda kuma a mafi yawan lokuta suke
gamuwa da masu garkuwa da mutane ko yan fashi ko kuma  a wasu lokutan su ci karo da jami’an tsaro.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Daliban da suka rubuta jarabawar JAMB sun nemi da a soke sakamakon da aka fitar

Wasu daga cikin daliban da suka rubuta jarabawar JAMB da ke ba da damar samun gurbin karatu a manyan makarantun gaba da sakandare ta shekarar...

Jam’iyyar ADC ta bugi kirjin kayar da gwamnatin APC ta Tinubu a zabe mai zuwa

Jam’iyyar African Democratic Congress ADC ta sha alwashin hada akalla masu kada kuri’a miliyan 35 domin kawar da jam’iyyar mai mulki ta APC da kuma...

Mafi Shahara