DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jirgin yakin soji a Nijar ya yi hatsari

-

Ministan tsaron jamhuriyar Nijar ne janar Salifou Mody ya sanar da faduwar jirgin mai saukar angulu na dakarun kasar a yayin da yake kan hanyar sa ta dawowa daga wani aikin sintirin hadin gwiwa da askarawan Burkina Faso
Sanarwar ministan ta ce da misalin karfe 12 na ranar Juma’ar nan ce 5 ga watan Janairu ne hatsarin jirgin ya auku sakamakon matsalar na’ura a daidai lokacin da yake shirin sauka a filin jirgin sojoji na Kantchari
Babu wanda ya rasa rai dai a wannan hatsari amma sai karamin rauni da mutum daya ya samu kamar yadda sanarwar ta ambato

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

INEC na duba buƙatun kungiyoyi 110 da ke neman rigista a matsayin jam’iyyun siyasa a Najeriya

Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewa ta karɓi wasikun buƙatun rajistar sabbin jam’iyyu 110 daga kungiyoyi daban-daban har zuwa Litinin, 23 ga watan...

PDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam’iyyar na kasa

PDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam'iyyar na kasa Jam’iyyar PDP ta dawo da Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyya na kasa bayan...

Mafi Shahara