DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Zargin kisan kai ya sa an tsare shugaban karamar hukuma gidan yari a Katsina

-

Kotun Majistare da ke zamanta a Katsina ta tsare shugaban karamar hukumar Batagarawa Alhaji Bala Garba Tsanni a gidan yari bisa zarginsa da kisa, satar mutum.
Ana zargin shugaban karamar hukumar tare da karin wasu mutane 11 da kisan Dagacin garin Dabaibayawa a cikin karamar hukumar Batagarawa ta jihar, Marigayi Alhaji Dikko Ahmad.
An dai gabatar da su gaban kotu ne karkashin sashe na 59, 249 da 189 na kundin penal code.
Tun da farko dai Alkalin kotun Majistare Abdulkarim A. Umar ya ba da umurni ga ‘yan sanda da su gabatar mata da wadanda ake zargi a ranar 25 ga watan Janairun, 2024.
Tsawon watanni 6 dai sauran mutanen 11 ke tsare a gidan yari, a yayin da aka ba da belin shugaban karamar hukumar.
Da suke gabatar da wadanda ake zargi da aikata wannan lamari, ‘yan sanda sun ce sun kammala bincike a kan batun.
A haka ne, Alkalin kotun ya umurci da a tsare shugaban karamar hukumar Bala Garba Tsanni a gidan yari har sai ranar 7 ga watan Maris mai zuwa na 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar...

Mafi Shahara