DCL Hausa Radio
Kaitsaye

J5 ta yi ajalin wani matashi bayan da kwastam suka biyo ta a Katsina

-

Wata mota kirar J5 ta yi sanadiyyar mutuwar wani matashi mai suna Mushin Ibrahim mai kimanin shekaru 14 a lokacin da birki ya kwace wa direban motar da yake gudun tsira bayan da jami’an kwastam suka biyo shi.
Lamarin kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, ya faru ne a makarantar firamaren Tudun Wada a Unguwar Tashar Huraira ta karamar hukumar Jibia a jihar Katsina a ranar Asabar din makon jiya.
Wani shaidar gani da ido ya ce jami’an na kwastam na zargin cewa wannan mota kirar J5 ta dauko kayan ‘sumoga’ ne yayin da suka yi kokarin kama ta.
Bayanai sun ce jami’an kwastam din na karkashin FOU shiyya ta B.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar...

Mafi Shahara