DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Dala na ci gaba da sauka, farashin kayan abinci ma na ci gaba da sauka a sassan Nijeriya

-

Dala na kara sauka, farashin kayan abinci na kara sauka a wasu kasuwannin Nijeriya.

A makon nan dai an sayi buhun masara a
kasuwar Mile 12 International Market dake Lagos an sayi buhun masara kan kuɗi ₦63,000, amma a makon da ya kare kuɗin buhun ₦65,000 ne, hakan na nuni da cewa an samu canjin ₦2000 kenan a kasuwar.
A kasuwar Mai’adua jihar Katsina ma an ɗan samu saukin ₦2000 kan kudin buhun Masara a wannan makon da muke shirin fita, inda aka sayi buhun kan kudi ₦62,0000 a satin nan, sai dai a makon da ya gabata kuwa ₦64,000 kuɗin kowane buhu na masara.
A makon da ya wuce an sayi buhun Masara ₦57,000 a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, hakan kuwa aka sai da a makon nan.
Sai dai, an sayar da buhun Masara ₦58,000 a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano a wannan makon, yayin da a wancan satin kuma aka saya ₦57,000,an samu karin dubu guda kenan kan farashin makon da ya shude.
Ita kuwa kasuwar Kashere da ke jihar Gombe, farashin buhun masara a wannan makon ya tashi sosai, a wancan makon dai an sayi buhun ₦52-53,000, amma a makon nan ₦60,000 daidai ne kuɗin buhun masarar.
Idan muka leka a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa kuwa, farashin bai sauya ba, an sayi buhun ₦59-60,000, haka nan zancen ya ke a makon nan da ke yi mana ban kwana ma.
Har ila yau, shinkafar Hausa ta fi tsada a kasuwar Karamar Hukumar Gerie da ke jihar Adamawa, a wannan makon, an sayi buhun shinkafar ₦143,000, amma a makon jiya kuma ₦139,000 kuɗin buhun yake, an samu karin ₦4,000 kenan a tsakanin kwanaki 7.
Amma farashin shinkafar bai canza zani ba a kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe, a makon da ya shude, ana sai da buhun ₦108-110- haka nan akwai na ₦115-120,000 ya dai danganta da kyan shinkafar, haka nan aka saya a wannan satin.
Da muka leka kasuwar Giwa ta jihar Kaduna kuwa, mun tarar da cewa kudin buhun shinkafar yana kamar yadda yake a satin can, an saya ₦128,000 satin da ya gabata, haka batun ya ke a satin nan ma .
Sai dai fa farashin shinkafar na ci gaba da sauka a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano sakamakon saukar Dala da CFA, an sayar da buhun shinkafar ₦120,000 a makon da ya gabata, yayin da a yanzu kuwa ake sai da ta ₦110,000 cif, an samu sassaucin ₦10,000 a makon nan.
A daidai lokacin da aka samu sauƙin ₦10,000 a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, ita kuwa kasuwar Mai’adua jihar Katsina kuɗin buhun ya fi na makon da ya shude tsada, inda a wancan aka sayi buhun ₦125,000, sai dai a makon nan ₦130,000 ne kuɗin buhun yake a kasuwar.
A kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos kuɗin buhun shinkafar ₦120,000 a wannan makon da ke dab da kare wa.
Kuɗin buhun shinkafar waje kuma ₦75,000 a kasuwar Mile 12 International Market dake Legos, sai dai shinkafar ta fi sauki a wasu kasuwannin Arewacin kasar, inda aka sayi buhun shinkafar ₦65,000 a kasuwar Mai’adua jihar Katsina wannan makon.
Ita ma kasuwar Dawanau da ke jihar Kano kuɗin buhun shinkafar baturen ya faɗi, a makon da ya shude an sai da buhun ₦83,000, yayin da a makon nan aka sayar kan kuɗi ₦75,000.
Hakan a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe ma kudin buhun shinkafar bature ya sauka sosai, an sayi buhun ₦75,000 makon nan, yayin da wancan makon kuwa aka sayar ₦80,000 daidai.
Sai dai a Kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa kuwa, farashin shinkafar bature ya sake tashi a wannan makon, inda aka sai da buhun ₦78,000 a satin nan, amma a makon da ya kare kuma ₦72,000 kudin buhun shinkafar, an samu karin kimanin ₦6,000 kenan.
An sayi shinkafar waje ₦78,000 a kasuwar Giwa dake jihar Kaduna a makon jiya, yayin da a wannan makon kuwa aka sai da kan kudi ₦75,000.
To bari mu ƙarƙare farashin kayan abincin na wannan makon da Taliyar Spaghetti.
To wannan makon ma farashin taliyar ya ɗan sauka a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, an sayi 
Kwalin taliyar kan kudi ₦14,000 a makon nan, sai dai a makon can ₦15,000 ne daidai kuɗin Kwalin taliyar.
Amma kasuwar Giwa dake jihar Kaduna kuwa kuɗin Kwalin taliya ₦14,500 ne a makon nan,₦14,500 ɗin aka saya makon da ya shude.
A kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, kudin Kwalin taliyar bai sauya ba daga na makon da ya gabata, an sayi kwalin kan kudi ₦13,200 a wancan makon, haka nan a satin nan ma.
Sai dai fa kasuwar Kashere na jihar Gombe Kwalin taliyar ya fi na makon da ya shude tsada, an sayi kwalin ₦13,000, amma a makon nan kuɗin Kwalin ₦13,200 ne.
A kasuwar Dawanau na jihar Kano ana sai da Kwalin taliya ₦13,500 a makon nan, haka nan a wannan makon ma.
Kwalin taliyar ya fi tsada a makon nan a kasuwar Mai’adua jihar Katsina, an sayi Kwalin ₦13,000 a makon da ya kare, yayin da a wannan makon dake dab da karewa aka sai da ta kan kuɗi ₦13,500

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Yan kasuwar mai sun sauke farashin man fetur kasa da yadda Dagote ke sayarwa

Wasu masu shigo da man fetur daga ƙasashen waje sun fara sayar da shi a ƙasa da Naira 860 kowace lita, lamarin da ya sauka...

Saurayi ya gaggabe wa budurwarsa hakora shida a Legas

Wani saurayi a unguwar Ibadan dake Ebute Meta, jihar Legas, ya lakadawa budurwarsa Fatima, wadda ke sana’ar gyaran kai, dukan da ya janyo ta rasa...

Mafi Shahara