DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun yi yunkurin kai harin ramuwar-gayya a Danmusa jihar Katsina

-

Wani rahoto da DCL Hausa ta samu na cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san adadinsu ba sun yi yunkurin shiga garin Danmusa, hedikwatar karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina cikin daren nan na Litinin.
Sai dai bayanai sun ce jami’an sun yi nasarar dakile wannan yunkuri hari da aka kira na ramuwar gayya. Yunkurin ‘yan bindigar ya biyo bayan wani aikin fatattakar ‘yan bindiga da jami’an tsaro aka sanar cewa sun yi a kauyen Katsira, inda bayanai suka ce jamian tsaro sun yi nasarar konawa tare da lalata mafakar ‘yam bindigar da dama.
Duk da dai a yayin samamen jami’an tsaron ba a ba da rahoton an kashe ko jikkata wasu ‘yan bindigar ba, amma wata majiya daga jami’an tsaro da ta nemi da kada a ambace ta, ta tabbatar da cewa an yi wa ‘yan bindigar barna mai yawa.
Hakan ne ma, kamar yadda majiyar ta sanar da DCL Hausa ya sa ‘yan bindigar suka yi zuga, da zummar ramuwar gayya a garin na Danmusa. Amma jami’an tsaro suka sake samun nasarar fatattakarsu.
Ya zuwa lokacin hada wannan labarin, mutanen garin na Danmusa dai sun firgita, da hakan ya sa har wasu suka fara tunanin ko ma ‘yan bindigar sun shiga garin, a lokacin da suka ji karar harbe-harben bindiga a bayan gari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar...

Mafi Shahara